Wednesday, 19 June 2019


[Zuwana Ƙasar Romaniya, daga Muhsin Ibrahim]

Tarihihi yana da muhimmanci wajen fahimtarmu game da al'amuran duniya. Jiya mun je Bucharest, babban birnin ƙasar Romania. Lokacin da muke hanya, na karanta bayanai game da wasu shugabannin Afirka masu kama-karya ƙarƙashin mulkin soja, kama daga Addis Ababa zuwa Bangui, daga Kampala zuwa Kinsasha, da dai sauransu. A lokacin, sai wani abu yai ta faɗo min a rai: me 'yan mulkin kama-karyar nan, waɗanda mulkinsu ya ƙaƙƙare a shekarun 1960 zuwa 1970, suke tunani ne yayin mulkinsu? To amma da muka je gida da babban zauren majalisar Nicolae Ceausescu, taƙadarin shugaban gurguzu na ƙasar ta Romania, sai kawai na fahimci komai.

Mulki ba ya ɗorewa. Mista Ceausescu ya mulki ƙasar na tsawon shekara 25. Ganin irin gine-gine da ya bari, ba za ka taɓa ɗauka yana tunanin mutuwa ba. Amma a Disambar 1989, kawai sai aka tayar da wata zanga-zanga, wacce daga baya ta yi sanadiyar karyewar mulkinsa da mutuwarsa tare da matarsa.

Waɗannan su ne hotunan da muka ɗauka a gidansa mai ɗakuna 80 da kuma zauren majalisar ƙasar, wanda shi ne ginin ma'aikata mafi girma a duniya bayan Pentagon. Zinare ne a ciki ta ko'ina, har a cikin ban-ɗakinsa mai kama da ɗakin kwana. Yau dai ni da mai ɗakina sai da muka bayyana cewa mu 'yan Najeriya ne, ba Congo ba, yayin da kowa ya juyo yana zura mana ido sa'ar da aka ambaci sunan Muboto.

Akwai ɗimbin darussa da za mu ɗauka cikin rayuwar waɗannan shaƙiyyan shugabanni. Idan mutum ya kalli rayuwarsu, zai yi saurin fahimtar yadda ƙarshensu yake kasancewa. Duniyar nan ba komai ba ce domin babu wanda babu mutuwa a kansa. Saboda 'yan baya, ka kasance wanda tarihi zai tuna nagartarka, a yayin da mu, a matsayinmu na Musulmi, mun yi imani cewa addu'a na binmu har bayan mutuwa.

Allah ya sa gabanmu ya fi bayanmu kyautatuwa.

*Muhsin Ibrahim ne ya rubuta wannan maƙala da Ingilishi sannan Muhammadu Sabiu ya fassara zuwa Hausa.

No comments:

Post a Comment